1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda auren-wuri ya raba yara mata da karatun boko a Katsina

November 8, 2022

'Yan mata da dama a Najeriya na kaurace wa karatun boko sakamakon auren-wuri da aka yi musu, lamarin da ke kawar musu da yunkurinsu na tallafa wa al'umma ta hanyar aikin likita da sauran ayyuka.

Nigeria Symbolbild | Mädchen auf dem Weg zur Schule
Wasu dalibai mata a jihar KanoHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

A wasu yankuna na arewacin Najeriya dai iyaye da dama na dakile wa mata burinsu na yin karatun boko ta hanyar cire su daga makarantu ayi musu aure tun suna kanana. Hakan ta faru ga Asma'u Abdullahi  wacce ta shaida wa DW Hausa cewa ta sha bakar wahala a lokacin da aka iyayenta suka cire ta daga makaranta suka yi mata aure. Ta ce babban abin da ya ba ta wahala a lokacin shi ne an aurar da ita ga gidan da akwai kishiya kuma ga 'ya'yan mjinta sun fara girma.

''Ina saura shekara daya na kammala karatun sakandare aka yi min aure, kuma auren ko watanni shida bai wuce ba ya mutu. Daga nan ban sake ci gaba da karatu ba.'' in ji Asma'u

Ita kuwa Aisha Muhammad ta shaida wa DW cewa auren-wurin da aka yi mata ya sanya ta ganin darasin rayuwa kala dabam-dabam. Ta ce '' ba na son mijin da aka aura min. Idan da an bar ni na kammala karatuna da watakila wahalar da mijin ya ba ni ba ta kai girman hakan ba, tun da wata bakwai auran namu ya yi ya mutu.''

Matsalar auren-wurin dai kan sanya wasu daga cikin yara mata cikin rayuwar kaskanci, inda Asma'u Abdullahi ta shaida wa DW cewa a lokacin da aka yi mata aure tana da kananan shekaru ba ma ta son abokan karatunta su gane cewa aure aka yi mata.