Umarnin kame daruruwan sojoji a Turkiyya
November 29, 2017A kasar Turkiyya an sake ba da umarnin kame daruruwan sojojin kasar da ake zargi magoya bayan fitaccen malamin kasar ne Fethullah Gülen. Wannan matakin da aka dauka a birnin Santambul, an mayar da hankali kan sojojin kasar, inji kamfanin dillancin labarun Turkiyya Anadolu. A jimilce ma'aikatar shari'ar Turkiyya ta ba da sammacin kame sojoji 360.
Shi dai babban malamin Fethullah Gülen da ke zaune a kasar Amirka, ana zarginsa da kulla makarkashiyar wani yunkurin juyin mulkin soji da bai yi nasara. Sai dai ya sha musanta wannan zargi.
Tun bayan yunkurin juyin mulki a watan Yulin shekarar 2016, an kame akalla mutane fiye da dubu 50 a kasar ta Turkiyya bisa zargin alaka da Gülen. An sako mutane dubu 150 da suka hada da jami'an soji da ma'aikatan gwamnati da kuma na kamfanoni masu zaman kansu.