UNESCO ta amince da al'adun gargajiya na tarihi
December 11, 2025
Talla
Hukumar raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da al'adu da dabi'u da dama daga dukkan sassan duniya a taron da ta gudanar karo na ashirin kan al'adun da al'umma suka gada na kaka da kakanni.
Taron na UNESCO ya gudana ne a birnin Delhi inda ya amince da bikin al'adu na Diwali na mabiya addinin Hindu.
Taron ya zayyana al'adu da dabi'u da fasahohi na gargajiya wadanda duka hukumar ta amince da su bisa fahimtar cewa fasaha ce ko Ilmi da ke neman bacewa.