SiyasaSudan
UNHCR na bukatar kudade saboda Sudan
September 4, 2023![](https://static.dw.com/image/66349407_800.webp)
Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar dala bilian daya domin kai agajin gaggawa ga mutane kusan miliyan biyu da ke kokarin gudun hijira a Sudan.
A bayanin da ta yi game da wannan batun, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar UNHCR ta ce kudaden da take son samu a wannan karon sun ninka har sau biyu daga adadin bukatar da ta gabatar a watan Mayu.
Miliyoyin 'yan kasar Sudan ne dai ke kokarin tserewa daga yakin basasar da ake gwabzawa tsakanin sojojin da ke gaba da juna a kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar dubban mutane, ko baya ga masu kokarin hijirar guje wa halin da ake ciki a kasar.