UNICEF: 2016 ta kasance mai muni ga yaran Siriya
March 13, 2017A kalla yara 652 ne suka rigamu gidan gaskiya a Siriya a shekarar 2016, abin da ya sanya shekara ke zama mafi muni ga manyan na gobe a wannan kasa a cewar Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a wannan rana ta Litinin.
Asusun ya ce yara 255 an kashesu ne a cikin makarantu ko kusa da makarantun a shekarar ta bara, sannan akwai yara miliyan daya da dubu dari bakwai da ba sa zuwa makaranta, daya cikin makarantu uku na kasar ba sa cikin yanayi da za a iya karantu a cikinsa saboda 'yan bindiga sun kwace su a cewar rahoton.
Har ila yau rahoton asusun ya kara da cewa akwai yara 'yan asalin Siriya miliyan biyu da dubu dari uku da ke neman mafaka a wasu kasashe da ke a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan adadi na yara da ke cikin garari ko ma suka halaka a cewar rahoton na UNICEF na zuwa ne kwanaki biyu kafin cikar shekaru shida da fara gangami da ya rikide zuwa yakin basasa a kasar ta Siriya.