UNICEF: Harin bama-bamai da yara na karuwa
April 12, 2017![Kongo Brazzaville Unicef Fehlernährung](https://static.dw.com/image/37939377_800.webp)
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadi da kakkausar murya kan yadda kungiyar Boko Haram ke kara amfani da yara musamman mata domin kai hare-haren bama-bamai na kunar bakin wake a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Asusun na UNICEF ya bayyana wannan gargadi ne a wani sabon rahoto na karshen watanni uku na farkon shekara ta 2017, UNICEF ya ce an kai harin kunar-bakin-wake kimanin 77 a Najeriya da kasashen Chadi, da Kamaru da ke makobtaka da Najeriya wadanda suka fi fama da hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin gabar Tafkin Chadi.
Tun daga shekara ta 2014 zuwa yanzu rahoton ya nuna cewa an yi amfani da kanan yara 117 wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake a wuraren taruwar jama'a kamar kasuwanni da wuraren ibada a kasashen Najeriya da Chadi da Nijar da kuma Kamaru.
A shekara ta 2014 da rahotanni suka nuna an samu hudu da aka fara amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake inda aka samu 56 a cikin 2015, da kuma 30 a shekara ta 2016.
Kimanin kananan yara 27 ne wannan rahoton ya nuna cewa Kungiyar ta Boko Haram tayi amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake daga watan Janairu zuwa watan Maris na wannan shekara abin da ya ke nuna cewa ana samun karuwar amfanin da yaran wajen kai hare-hare.
Sai dai a wata tattaunawa da aka yi da kwamishinar kula da harkokin mata ta jihar Borno Hon Fanta Baba Shehu ta ce mataki daya ne za a bi a magance wannan matsalar shi ne na ilimantar da mata da yara. Babbar jami'ar Asusun UNICEF mai kula da Nahiyar Afirka ta Yamma da kuma Afirka ta Tsakiya Marie-Pierre ta bayyana a cikin wannan rahoton cewa wannan shi ne cin zarafin yara mafi muni da aka taba samu a rikice-rikice a fadin duniya.