1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF ta ja hankali kan mahimmancin tsafta

Abdurrahman Kabir daga KanoDecember 10, 2014

Mata ne zalla ke bi gida gida suna wayar da kai dan wayar da kai kan tsabtar da ake son matan karkara su koya ta jikinsu musamman a lokacin jinin al’ada.

UNICEF verliert laut Medienberichten das Spendensiegel des DZI
Hoto: AP

Ofishin Asusun Tallafin kananan yaran UNICEF zai yi makwanni uku yana wayar da kan matan karkarar kanan hukumomin Takai da Madobi kan tsabtar hannu wajen riga kafi kamar yadda shugabar shirin Hajiya Sa'a Ibrahim Magashi ta yi Karin haske a kai:

“Ita harkar wanke hannu bincike ya nuna cewa cututtuka da dama suna shiga jikin mutane ne ta abincin da muke ci da hannayenmu. Shi ya sa aka dauko wannan kamfe daga tushe cewa lalle iyali su gane muhimmancin wanke hannu. Shi kuma wanke hannun nan akwai lokutan yinsa. Duk lokacin da mutum zai ci abinci, lokacin da mutum ya shiga ban daki, lokacin da mace mai shayarwa za ta hada abincin yaro.”

Wanke hannu ba bakuwar al'ada ba ce sai dai sai dai yadda za a yi riga kafin cututtukan ne ke bukatar wayar da kai kamar yadda Malam Tijjani Ja'afar masani kan tsabtar jiki ya bayyana.

'“Za ka dauko sabulu ka saba sabulun nan a hannunka ka mutstsika tafukan hannu, sannan ka juya hannun daya ya wanke bayan daya ka kara juyawa daya ya wanke bayan daya sannan ka tsattsefe dukkan tsakanin ‘yan yatsun ka da dukkan wani yanka dake jikin hannu ka tabbata ka mutstsika shi kuma abin ya yi kumfa. Sannan idan ka yi wannan sannan za ka yi kokarin ka saka kan furtunanka a tsakiyar tafin hannunka ka goggoga sannan sai a zuba maka ruwa mai gudana inda zai wanke”.

Hoto: Reuters

Wata kuma tsabtar da ake son matan karkara su koya ita ce ta jikinsu a lokacin jinin al'ada.A wannan shiri mata ne zalla zasu bi gida gida suna wayar da kai. Hajiya Sa'a ta bayyana ta bayyana abin da wannan wayar dai zai kunsa.

Bisa al'ada mace ba ta yarda a ga tsummanta na al'ada saboda da haka idan aka je aka wanke shi zuwa ake a sami gefen gado wanda yake daga kurya sai a je a saka tsumman a wurin da danshinsa.To yanzu sai bincike ya nuna cewa kwayoyin cuta su kan kasance a jikin wannan tsumma matsawar ba a busar das hi ya bushe karau ba.”

Hoto: UNICEF

Akwai cutuka da dama da a yanzu haka tsabta ce riga kafinsu da a yanzu haka hukumomin lafiya da kungiyoyi ke matsa kaimin yaki da su ta wannan siga.