UNICEF: Yara da dama na fama da yunwa
February 21, 2017![Matsalar yunwa a tsakanin kananan yara](https://static.dw.com/image/18616246_800.webp)
Wadannan kasashe dai sun hada da Najeriya da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma Yemen, inda babban daraktan asusun ya ce muddin ba a dauki wasu matakai na gaggawa ba to tabbas yara za su kara shiga halin ni 'yasu. Rahoton na asusun ya nunar da cewa a kasar Yemen, inda ake fama da yakin basasa kusan shekaru biyu yara dubu 462 ne ke fama dayunwa mai tsanani, yayin da a Najeriya a yankunan da ake fama da rikicin Boko Haram ake da yara dubu 450 da ke cikin wannan mawuyacin hali na rayuwa.
Matsalar fari a Somaliya ta bar yara dubu 185 da ke daf da fadawa matsalar yunwa, kuma adadin na iya kai wa dubu 270 nan da 'yan watanni masu zuwa, yayin da a Sudan ta Kudu yara dubu 270 ne ke fama da matsananciyar yunwar. Babban daraktan asusun na UNICEF Antony Lake ya yi kira da a dauki matakan gaggawa.