1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF:Yara na hallaka a kasashen da ake yaki

Gazali Abdou Tasawa
December 28, 2017

Wani rahoto da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya fitar ya nunar da cewa a Najeriya da sauran sasan duniya masu fama da yaki yara da dama na mutuwa wasu na jin raunika.

Wata karamar yarinya kenan a sansanin 'yan gudun hijirar Boko Haram a Maiduguri
Wata karamar yarinya kenan a sansanin 'yan gudun hijirar Boko Haram a MaiduguriHoto: picture alliance/dpa/Unicef/NOTIMEX


Wasu alkalumma da wannan rahoto ya fitar sun nuna cewa akwai kimanin yara dubu 350 da ke fama da bakar yunwa da karancin abinci mai gina jiki a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya wanda ake alakantawa da rikicin Boko Haram. Asusun na UNICEF ya nuna cewar ana kai hare-hare kan yara da saka su cikin hadarin mutuwa ko na jikkata a gidajensu ko makarantu ko wuraren wasanninsu.

Rahoton ya ci gaba da cewa a shekara nan da ke karewa alkaluma sun nuna cewa a kasashen Najeriya da Kamaru, kungiyar Boko Haram ta tilasata wa kimanin yara 135 kai hare-haren kunar bakin wake, wanda ya ninka so biyar na yaran da kungiyar ta yi amfani da su wajen kunar bakin wake a shekara ta 2016. Rahoton wanda darakta mai kula da shirin agaji na cibiyar Mr. Manuel Fontaine ya wallafa, Asusun na UNICEF ya nuna cewa ana amfani da yara a matsayin garkuwar yaki ana cin zarafinsu ana musu fyade tare da hallaka su a fagagyen daga.

Hoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

A cewar UNICEF yara da 'yan bindiga dadi suka sace suna gamuwa da cin zarafi ta kowane fanni inda ko an tseratar da su sun koma hannun jami'an tsaro, akwai zargin ana gallaza musu tare da keta musu haddi. Hakan yana nuna irin yadda bangarorin da ke gwabza yaki suka yi watsi da dokokin kasa da kasa wadanda aka tsara domin kare masu rauni a cikin al'umma. Sai dai a cewar Sama'ila Idris Hina wani jami'in aikin agaji a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, Sojojin kam na kokarin kare dokokin yaki, matsalar na ga bangaren mayakan Boko Haram.

Bisa lura da abubuwa da ke faruwa a sansanonin 'yan gudun hijira da ma manyan garuruwan jihohin Borno da Yobe da Adamawa wadanda sune suka fi fukantar matsalar yaki da Boko Haram, yara na matukar fuskantar baranazana wacce ka iya lamushe rayukansu. Banda amfani da su wajen kai hare-haren da kai musu hare-haren kai tsaye, dubban yara na fama da yunwa ga rashin muhalli da rashin samun damar yin karatu inda yanzu haka dubbai suke ayyukan kwadago domin neman na sa wa a bakin salati ko taimakawa iyalansu. Akwai kuma matsalar fyade wacce ta zama ruwan dare gama duniya da ma sace yara ana ayyukan tsafe-tsafe da su.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Asusun na UNICEF ya yi kira ga bangarorin da suke bin ka'idodji da yarjejeniyoyi na yaki tare da tabbatar da kare yara da fitar da su daga duk wata barazana da suke fuskanta inda kuma ta yi kira ga hukukomin da su matsa kaimi wajen ganin an kare dukkanin yara daga hadarin da suke fuskanta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani