1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNITA a Angola za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓe

September 2, 2012

Babbar jam'iyyar addawa ta ƙasar Angola UNITA ta ce ta na shirin gabatar da koke a gaban hukumar zaɓe dangane da sakamakon da ta baiyana na zaɓen 'yan majalisun dokoki.

Isaias Samakuva, leader of Angola's main opposition UNITA party , addresses supporters during the party's last rally ahead of parliamentary elections in Viana, about 30 km (19 miles) east of the capital Luanda, August 29, 2012. Angolans will go to the polls on Friday to elect lawmakers and their president. REUTERS/Siphiwe Sibeko (ANGOLA - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Wani kakkakin jam'iyyar ya ce suna da takardun na shaidu, da suka tattara daga rufunan zaɓe inda suke da wakilai ,wanda ke nuna cewar sakamakon da hukumar ta baiyana ba shi ba ne ke cikin hannun wakilan su.

Sakamakon wuccin gadi da hukumar ta baiyana na nuna cewar jam'iyyar yan addawar ta UNITA na da kishi 17 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa. Yayin da jam'iyyar da ke yin mulkin ta MPLA ta sami kishi 74, abin da ke baiwa shugaba José Eduardo Dos Santo damar yin wani sabon wa'adin na mulki.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe