1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Zanga-zangar kan sahihancin zaben Venezuela

Suleiman Babayo ZMA
July 30, 2024

Sabuwar zanga-zangar adawa da sahihancin sakamakon zaben shugaban Venezuela ta barke inda mutum guda ya rasa ransa lokacin artabu da jami'an tsaro.

Venezuela Zanga-zanga
Zanga-zangar adawa da sahihancin sakamakon zaben shugaban VenezuelaHoto: Jesus Vargas/Getty Images

Mutum daya ya halaka lokacin zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaben kasar Venezuela da ya sake dawo da Shugaba Nicolas Maduro kan madafun ikon kasar da ke yankin Latin Amirka, a karo na uku a jere. Sabuwar zanga-zangar wadda ta barke a wannan Talata ta janyo artabu tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.

Dubban mutane suna ci gaba da fantsama kan tituna domin nuna dawa da sahihancin zaben da suke zargin an tafka kazamin magudi.

Da wannan sakamakon zaben da ake tababa ya nuna Shugaba Nicolas Maduro na kasar ta Venezuela mai shekaru 61 da haihuwa ya sake samun damar ci gaba da mulki na karin shekaru shida masu zuwa.