1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Dan Fodio: Ya samar da Daular Sokoto

June 17, 2021

Ya kasance malamin addini da ya jagoranci juyin-juya hali: Usman dan Fodio da ake wa al'kunya ta ladabi da Shehu, ya yi suka ga sarakuna tare da kawo sauyi a tsarin siyasa a yankin da yanzu ya kasance arewacin Najeriya.

DW African Roots | Sheikh Usman dan Fodio

Mene ne asalin Shehu Usman Dan Fodio?

An haifi Shehu Usman Dan Fodio a ranar 15 ga watan Disambar shekara ta 1754 a kauyen Maratta, da ke garin Gobir na al'ummar Hausa, inda yanzu ya kasance arewacin Najeriya. Ya karanta fannin shari'a da ilimin fikihu da kuma falsafa a Agadez (inda yanzu ke cikin Jamhuriyar Nijar) a gaban malamin addinin Musulunci Jibril Ibn Umar. Sakamakon iliminsa na addini da karfin fada a ji da yake da shi, daga bisani ana kiransa da inkiyar girmamawa ta Shehu Usman.

Ya aka yi Usman Dan Fodio ya kalubalanci tsarin gudanar da mulki?

Bayan ya kammala karatunsa, ya koma Gobir, inda ya fara yi wa mutane wa'azin addinin Musulunci, wadanda a wancan lokaci ke cakuda rashin addini da Musulunci. Ya yi fice sosai a Gobir, inda har sarkin Gobir na wancan lokaci Rimfa yake ganin Usman Dan Fodio a matsayin barazana ya kuma yi kokarin halaka shi. Dan Fodio ya tsere, inda ya fara gwagwarmaya a tsakanin al'ummomin yankunan karkara ta hanyar wa'azi da koyarawa da kuma rubutu.

A shekara ta 1803 Shehu Usman da daruruwan mabiyansa, sun yi hijira zuwa Gudu, inda ya ci gaba da yada addinin Musulunci. Yayin da yake Gudu, Usman Dan fodio ya kaddamar da jihadi a kan Sarki Yunfa na Gobir (dan tsohon Sarki Rimfa da ya gaje shi) da mutanensa da yake ganin rayuwarsu ta saba da koyarwar addinin Musulunci.

Ta yaya Usman Dan Fodio ya kafa Daular Sokoto?

Kaddamar da jihadin ya yadu a kasar Hausa, inda mutane da dama suka bugi kirji suka shiga cikin rundunarsa. A shekara ta 1804, ya bayyana kaddamaar da jihadi a baki dayan kasar Hausa. A shekara ta 1808, Shehu Usman da mabiyansa sun kame Gobir da Kano da kuma wasu garuruwan Hausa. Ya ajiye makamansa a shekarar 1811, inda ya koma koyarwa da kuma rubutu, sai dai sojojinsa sun ci gaba da kame garuruwa har shekara ta 1815.

Tushen Afirka: Tarihin Usman Dan Fodio

02:11

This browser does not support the video element.

Juyin-juya halin Musuluncin ya hada kan yankunan Hausawa a karkashin shari'ar Musulunci, abin da ya jagoranci kafa Daular Sokoto a shekara ta 1812. Daular ta kunshi manya da kananan masarautu, wadanda da damansu suka maye gurbin sarakunan Hausawa na da.  Daular Sokoto ta kasance mafi karfin tattalin arziki da siyasa a yankin cikin karni na 19. Ta taimaka gaya wajen fadada yaduwar Musulunci a arewacin Najeriya.

Wanne muhimmanci Daular da Usman Dan Fodio ya samar take da shi?

Daularsa ta addinin Musulunci ta kunshi bangare da dama na inda ake kira yankin arewacin Najeriya da wani bangare na Jamhuriyar Nijar har ma da arewacin Kamaru. Jihadin ya bayar da kwarin gwiwa ga jerin yake-yake da sunan jihadi a Afirka ta Yamma, a wannan lokaci Musulunci ya kasance mafi rinjayen addini tsakanin al'ummar Afirka ta Yamma.

A shekara ta 1827, Daular Sokoto da ke da yawan al'umma kimanin miliyan 20, ta zamo Daula mafi yawan al'umma a Afirka ta Yamma. 

Shehu Usman Dan Fodio ya rasu a ranar 20 ga watan Afirilu na shekara ta 1817 a Sokoto.

Wadanda suka taimaka da shawarwari wajen rubuta wannan tarihi sun hadar da Farfesan tarihi Doulaye Konaté da Dr. Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel  ce ta taimaka wajen kawo muku Tushen Afirka.