1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaItaliya

An bizne gawar Fafaroma a Cocin Basilica

Abdoulaye Mamane Amadou AH
April 26, 2025

Dubun dubatar mutane mabiya Addinin Kirista sun yi cikar kwari a jana'izar karshe da ake yi wa jagoran darikar Katolika Fafaroma Francis, a cikin yanayi na matakan tsaro.

Hoto: Dan Kitwood/Getty Images

Hukumomi a birnin Roma sun tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen St. Peter's Square na fadar Vatican inda ake gudanar da jana'izar Fararoma Francis. Tun da sanyin safiya dubun dubatar jama'a suka yi wa dandalin cikar kwari domin samun damar yi wa Fafaroma Francis ganin karshe a jana'izar da ke zama guda a cikin mafi girma a duniya.

Fafaroma ya rasu bayan ya yi fama da doguwar jinya

Shugabannin manyan kasashen duniya ciki har da na Faransa da Amurka da wasu jagororin gwamnatoci ciki har da na Jamus da Burtaniya da fitattun sarakunan duniya irinsu na Jordan, duk sun halarci jana'izar. Shugaba Putin bai samu halartar jana'izar ba, amma kuma takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ya halarta dandalin na St. Peter's don yi wa Fafaroma Francis ganin karshe.

Fafaroma Francis ya yi addu'ar Easter duk da rashin lafiya

Ana jana'izar na zuwa ne bayan kammala yi wa gawar Fafaroma ganin bankwana na tsawon kwanaki da wasu dubban mabiya darikar ta Khatolika suka yi a cikin yanayi na juyayi da alhini.