1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi bankwanan karshe da Paparoma

January 5, 2023

Fadar Vatikan aka yi jana'iza tare da bankwanan karshe wa Paparoma Benedik na 16, wanda ya rasu a ranar Asabar din da ta gabata yana mai shekaru 96 da haihuwa.

BG - Beisetzung Papst Benedikt
Hoto: GUGLIELMO MANGIAPANE/REUTERS

Bikin jana'izar ya samu halartar shugabanni addini mabiya darikar Katolika da shugabannin gwamnatoci da kasashe da kuma dumbin mabiya daga sassa daban daban na duniya, ciki har da shugaban gwanantin Jamus Olaf Scholz.

Shagulgulan jana'izar ya gudana ne a karkashin Paparoma Francis wanda ya karbi jagorancin fadar Vatikan daga hannun marigayi Benedikt na 16, bayan ya kafa tarihi na zama jagoran darikar katolika  na farko da ya yi marabus a shekarar 2013.

Karin bayani: Mutuwar Benedict na 16 ta girgiza shugabannin duniya

Bayan isowarsa gurin a kekan guragu yana kewaye da kadinal 5, Paparoma Francois ya yi mubaya'a wa gawar wacce ke cikin bakin akwati mai dauke da sunan marigayin na asali da kuma Bible.

Marigayi Benedict XVI na nadin sabon Cardinal Joseph Zen Ze-KiunHoto: Maurizio Brambatti/epa/ansa/dpa/picture-alliance

"Mun zo a nan da turare mai tsarki don nuna wa marigayin soyayyarmu a gare shi wacce ba za ta taba fita ba daga zukatanmu. Za mu numa masa kauna marar misali cikin girmamawa kamar yadda ya share shekaru masu yawa yana nuna irinta tare da hidimtawa wannan addini. Sai mu ce ya  Allah mun mi ka ruhin sa a gareka".

An kwashe sama da awa daya ana addu'a wa gawar wacce sama da limaman cocin 4,000 suka jagoranta, kuma shi ne karon farko a tarihin  da wani fafaroma ya halarci jana'izar wani fafaroma. Ga mabiya addinin Krista wadanda suka samu halarta jana'izar bajamushen Fafaroman.