Vatikan ta Zabi Robert Prevos a matsayin Fafaroma
May 9, 2025
Yanzu haka dai ana jiran a bayyana sunan sabaon shugaban darikar Katolika na duniya, yayin da farin hayaki ya tirnike bututun hayaki na cocin Sistine da ke fadar Katolika. A cewar kamfanin dillancin labaran Italiya Ansa, an zabi sabon fafaroma a zagaye na hudu na zaben. Da yammacin Laraba ne aka fara taron na Kadinal 133 domin zaben wanda zai gaji marigayi Fafaroma Francis.
'Yan takarar zama fafaroma daga Afirka: Akwai fata kan samun Fafaroma daga Afirka
Bayyanar farin hayaki ta bututun saman rufin cocin Sistine da ke fadar Vatikan ce ta nuna nasarar zabin wanda zai jagoranci mabiya darikar mutum biliyan daya da miliyan 400 a duniya. Marigayi Fafaroma Francis ya mutu a ranar Ista: Gawar Fafaroma Francis ta isa cocin St Peter domin ban-kwana
Dubun dubatan mabiya a dandalin St. Peters da ke dakon samun sakamakon zaben, sun yi ta sowar murna da farin ciki kan samun sabon jagora na darikar a duniya. Wannan ne karo na farko da ake samun zaben sabon fafaroma daga Amurka. Kuma an kai zagaye na hudu cikin kwanaki biyu kafin a cim ma nasarar zabo sabon fafaroman.