1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVenezuela

Venezuela: Shugaba Maduro ya lashe zabe karo uku

July 29, 2024

Hukumar zabe a Venezuela, ta tabbatar da shugaban kasar, Nicolás Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kammala. A shekara ta 2018 ne Mr. Maduro ya lashe zabe a wa'adi na biyu.

Shugaba Nicolas Maduro na Vanezuela
Shugaba Nicolas Maduro na VanezuelaHoto: Fernando Vergara/AP Photo/picture alliance

Hukumar zaben ta ce Shugaba Nicolás Maduro ya lashe zaben ne da kashi 51% na kuri'un da aka kada, kuma wanda ya biye masa shi ne Edmundo González da ya samu kashi 44%

'Yan takara 10 ne dai suka ffata a zaben na na Venezuela, inda kuri'un jin ra'ayin jama'a gabanin zaben ya nuno Edmundo González din a gaban Shugaba Maduro.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa gwamnatin kasar ta kama da dama daga cikin 'yan hamayya yayin da ake haramar zabe.

Shekaru 11 ke nan yanzu Nicolás Maduro ke mulki a Venezuela da ke yankin kudancin Amurka.

A shekara ta 2018 ne Mr. Maduro ya lashe zabe a wa'adi na biyu, zaben kuma da ya sha suka saboda saba wa tsari na dimukuradiyya.