Venezuwela ta saki dan jaridar Jamus
March 16, 2019Talla
Wata kungiyar kare 'yancin 'yan jaridu a Venezuwela ta tabbatar da sakin dan jaridar Jamus Billy Six da hukumomi suka tsare kan zargin leken asiri da yi wa gwamnati zagon kasa. Kungiyar Espacio Publico ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an saki dan jaridar ne bisa sharadin zai rika gabatar da kansa ga hukumomi duk bayan kwanaki 15 tare da haramta masa yin magana kan halin da ya shiga bayan da shafe watanni hudu a tsare a kurkuku.
Billy Six dan jarida ne mai aiko da rahotanni na wata mujalla a Jamus, ya kuma shahara a rahotannin yankunan yaki cikin har da kasashen Libiya da Ukraine da Siriya.