Vladimir Putin ya lashe zaben Rasha
March 4, 2012Firaministan Ƙasar Rasha wato Vladimir Putin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa sakamakon samun gagarumin rinjaye da ya yi tun a zagayen farko da ya gudana a wannan lahadin. Alƙaluman da hukumar zaɓen ƙasar ta bayar sun nunar da cewar Putin ya lashe kashi 62,844% na ƙuri'un da aka kaɗa. Yayin da Guennadi Ziouganov da ke biya masa baya ya tashi da kashi 17,82 % na jimillar ƙuri'in. Sai dai ya zuwa yanzu kashi 15 % na ƙuri'un da aka kaɗa ne hukumomi suka yi nasarar tantancewa. Tun da farko ƙididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar tsakanin waɗanda suka kaɗa ƙuri'unsu ta nunar da cewar haƙar Putin za ta cimma ruwa.
Shi dai Putin mai shekaru 59 da haihuwa ya taɓa mulkar Rasha daga shekara ta 2000 zuwa ta 2008 kafin ya sauka, tare da riƙe mukamin firaminista. Sabon shugaban na Rasha wanda tsohon shugaban hukumar lekan asirin ta KGB ne, ya yi amfani da batun samar da kwanciyar hankalin ƙasa da kuma bunƙasar tattalin arziki a matsayin ginshiƙin yaƙin neman zaɓensa. 'Yan takara huɗu ne dai suka ƙalubalance Putin ciki kuwa har da wani attajiri mai suna Mikhail Prokhorov.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal