Vladimir Putin ya taya Merkel murna
December 17, 2013Talla
Angela Merkel wacce ta sha rantsuwar kama aiki a yau bayan da majalisar dokokin Bundestag ta sake zaɓenta a mattsayin sugabar gwamnatin a karo na uku da gaggarumin rinjaye.
Putin ya ce sake zaɓen nata, na tabbatar da hamzari da kuma jan aikin da ta yi a cikin shekaru na baya-baya nan,sannan ya ce duk da cewar Rasha tana da saɓanin tsakaninta da ƙasashen Ƙungiyar Tarrayar Turai a kan Yukren amma ya ce yana fatan Jamus za ta ƙara ƙarfafa hulɗa da Rasha. A cikin 'yan majalisun 631 , 462 suka amince da sake zaɓen shugabar gwamnatin. A farkon wannan mako ne aka cimma yarjejeniyar ta kafa gwamnatin ƙawance tsakanin jam'iyyun siyasa na CDU da CSU da kuma SPD.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu