1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Volkswagen zai rage ayyuka 50,000

Abdul-raheem Hassan
March 10, 2026

Katafaren kamfanin kera motoci na Jamus Volkswagen zai rage guraben ayyuka 50,000 a cikin gida nan da shekara ta 2030 sakamakon asara mafi girma a cikin shekaru 10.

Matakin da kamfanin ya dauka na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin wanda ke a matsayi na 10 ke fama da gasar tsere da motocin China masu aiki da laturoni da kuma harajin Amurka da kuma tsadar kayayyaki.

A cikin wata wasika da shugaban kamfanin Volkswagen Oliver Blume ya aikewa masu hannun jari a cikin rahoton shekara-shekara na kamfanin ya ce "A gaba daya, kusan ayyuka 50,000 ne za a katse nan da shekarar 2030 a ma'aikatun kamfanin Volkswagen da ke cikin Jamus."

Tuni dai kungiyar ta kulla yarjejeniya da kungiyoyin kwadago a karshen shekarar 2024 don rage ayyukan yi 35,000 nan da shekarar 2030 a matsayin wani bangare na tsare-tsaren ceto euro biliyan 15 a shekara.

Blume ya kara da cewa karin ragi zai fito ne daga man'yan kamfanoni na Audi da Porsche da kuma kamfanin Volkswagen na Cariad.

Tun ma kafin Shugaban Amurka Donald Trump ya saka haraji kan masu kera motocin kasashen waje, Volkswagen na fuskantar kalubale guda uku wadan da suka hada da matsananciyar bukatu a Turai da tsadar saka hannun jari a motocin laturoni wato EVs da kuma karuwar asara a China.

Volkswagen, wanda ya zama zakaran gwajen dafi a kasuwannin motoci a China kuma mafi girma a duniya, yana kokawa da gogayya mai tsanani daga sauran kamfanonin kera motoci a cikin gida, kuma tana fuskantar mumunar faduwa a China saboda motocin BYD da Geely.

Blume ya shaidawa taron manema labarai cewa, masu kera motoci na kasar Sin dake sa ido a kasuwannin Turai don samun mafita, zai kara matsin lamba ga kamfanin Volkswagen. "Muna bukatar mu shirya kanmu domin za mu fuskanci matsin farashin a nan," ya kar da cewa "Wannan babban abin ƙarfafawa ne a gare mu don yin aiki tukuru a kan farashi."