1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Von der Leyen ta samu wa'adi na biyu na jagorancin EU

Muntaqa Ahiwa Salihu Adamu Usman/Mouhamadou Awal
July 18, 2024

Majalisar dokokin Kungiyar Tarayyar Turai ta kada kuri'ar amincewa da Ursula von der Leyen a matsayin wacce ta samu wa’adi na biyu na shugabancin hukumar zartaswa EU, duk da matsalolin da ta vfuskanta a wa'adin farko. .

Von der Leyen ta yi godiya ga 'yan majalisar Eu da suka bata sabuwar dama
Von der Leyen ta yi godiya ga 'yan majalisar Eu da suka bata sabuwar damaHoto: Johannes Simon/Getty Images

Von der Leyen ta yi alkawarin inganta tsaro da masana'antu da kuma magance matsalar gidaje a kasashen Kungiyar Tarayyar  Turai. Tsohuwar ministar tsaro ta Jamus wacce ta zama mace ta farko da ta shugabanci hukumar EU tun a shekarar 2019 ta nuna kwarewa wajen jan ragamar hukumar tun da ta fara jagorantarta. A jawabin da ta gabatar a gabanin zabe, Ursula von der Leyen ta shaida wa ‘yan majalisar Turai cewa batun makomar nahiyar na sama da komai, kuma hakan ya dogara a kan mataki da suka dauka a duniyar da ke cike da tarin wahalhalu. 

von der Leyen za jadadda manufar Turai ta tsintsiya madaurinki dayaHoto: Jean-Francois Badias/AP/picture alliance

Ta ce: "Na saurari jiga-jigan dimukuradiyya na wannan majalisar cikin tsanaki, na kuma gamsu cewa ka'idojin da aka gabatar sun nuna kamanceceniyar da ke a tsakaninmu ne a tafiyar dimukuradiyyar ba kuma bambanci ba. Don haka abin da ya kamata mu fifita ya ‘yan uwana ‘yan majalisa, shi ne ci gabanmu da kuma gogayya da duniya."

Karin bayani:Jagororin EU sun amince da kara wa von der Leyen wa'adi

Shekaru biyar na jagorancin hukumar Turan da Ursula Von de Leyen ta yi sun gamu da manyan matsaloli irin su annobar Corona da yakin da Rasha kaddamar a kan Ukraine da ma tsadar makamashi da sauran kayayyaki. A karshen watan Yunin da ya gabata ne shugabannin Tarayyar Turai suka amince da takarar Ursula Von de Leyen a birnin Brussels na kasar Belgium

Ursula von der Leyen ta jaddada goyon bayanta ga Ukraine duk da ziyarar da Firaministan Hungary Victor orban ya kai Rasha a baya-bayan nan. Sannan ta ce jagorancinta idan ya dore, to tabbas za ta tsaye wajen kare muradu da tsarin rayuwar al'umar Turai..

'Yan majalisar Turai sun yi jerin gwano wajen zaben shugabar hukumar zartarwa ta EUHoto: Johannes Simon/Getty Images

Ta ce: " Ba zan zuba ido ina iana ganin tsananin rarrabuwar kai ya samu zama a tsakaninmu ba. Ba kuma zan yarda da manufofin masu akidun son zuciya da masu tsattsauran akidu sun lalata mana tsarin rayuwarmu ta Turawa ba. Kuma na tsaya a gabanku a yau a shirye domin jagorantar gwagwarmaya tare da taimakon jiga-jiganmu na dimukuradiyya a wannan majalisa."

Karin bayani: Majalisar EU na shirin bai wa Von der Leyen damar zarcewa

A jawabin da ta gabatar a ranar Alhamis gabanin zabe, ta shaida wa ‘yan majalisar Turai batun makomar nahiyar na sama da komai kuma hakan ya dogara a kan mataki da suka dauka a duniyar da ke cike da tarin wahalhalu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani