Zirin Gaza: Wa zai sake gina yankin?
December 14, 2023Kididdigar farko ta nuna kila za a kashe dalar Amurka biliyan 50, sai dai matsalar ita ce Zirin Gaza da sauran yankunan Falasdinawa na bukatar fiye da tallafin kudi da ayyukan gina yankin. Duk da cewar ana ci gaba da gwabza fada da mace-mace da rusa gine-gine, tuni takaddamar kudi ta barke. Babu cikakken adadin yawan rayuka da aka rasa a Gaza, haka ma kudin da ake bukata na sake tayar da gine ginen da bama-baman Isra'ila suka rusa.
Karin Bayani: An sako wasu da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza
Har yanzu dai Isra'ila ba ta fitar da wani shiri na wanda zai mulki Gaza idan har ta samu nasara a burinta na rusa Hamas ba, sai dai Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi watsi da duk wani yunkuri na mika mulkin yankin ga gwamnatin Falasdinu. Amma tuni ya riga ya yi magana kan batun sake gina Gaza, a wannan makon ne kafafen yada labaran Isra'ila suka ruwaito cewa ya shaida wa 'yan siyasar Isra'ila Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce a shirye suke wajen daukar nauyin sake gina Zirin Gazan. To sai dai manazarta da masu sharhi kan siyasar yankin Gabas ta Tsakiya kamar Nathan Brown na ganin cewa, kudi ba shi da tasiri sosai idan har ana muradin warware wannan rikici.
An bayar da shawarar cewa Turai ce za ta dauki nauyi kasancewar kungiyar Tarayyar EU musamman Jamus, sune manyan masu bayar da agaji na dogon lokaci ga yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Amurka ita ma daya ce daga cikin manyan masu bayar da gudummawa, kuma mai yiwuwa a yi kira kan tallafawa aikin sake ginin. Sai dai an ruwaito cewar a Amurka da Turai a bayan fage masu yanke shawara sun riga sun tambayi dalilin da ya sa za su sake amfani da miliyoyin kudin masu biyan haraji, domin sake gina abubuwan more rayuwar da watakila za a sake jefa musu bam-bamai a nan gaba. A cewar Yara Asi ta cibiyar Larabawa da ke Washington DC ba nan ne ma gizo ke sakar ba, sai dai yanayi na mamaye da nuna karfin iko da Isra'ila ke yi.
Karin Bayani: Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas
Haka kuma ana ta kiraye-kirayen cewa, Isra'ila ta biya kudin irin asarar da ta tafka a yakin da take yi a zirin Gaza. Wasu ke ganin saboda kallon da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da sauran kungiyoyin kasa da kasa ke mata a matsayin mai mamaye a yankin, ya kamata alhakin sake gina yankin ya rataya a wuyanta. A shekara ta 2010, Isra'ila ta amince da biyan diyya ga Hukumar ba da Agaji ga 'Yan Gudun Hijirar Falasdinu a Gabas ta Tsakiya ta Majalisar Dinkin Duniya dalar Amurka miliyan 10 da dubu 500, domin gine-ginen da aka lalata a lokacin karamin rikicin da ya barke a 2009 a yankin abin da ya janyo cece- ku ce tsakanin al'umma.