Wa'adin sulhu tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
July 27, 2012Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar gamaiyar Afirka sun baiwa ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu wa'adin na da 2 ga watan Augusta su warware saɓanin dake tsakaninsu. Sai dai kuma akwai batutuwa da dama waɗanda da kamar wuya bangarorin biyu su iya cimma daidaito akansu. Waɗannan kuwa sun haɗa da rabon dukiyar da aka samu daga albarkatun mai da batun kan iyakoki da kuma al'amuran tsaro. A dangane da wannan ƙiƙi-ƙaƙa na Sudan da Sudan ta Kudu kwararrun masana na ƙasa da ƙasa da manazarta al'amuran yau da kullum da jami'an ayyukan raya ƙasa suka hallara a nan Bonn inda suka yi bitar matsalolin.
Muhimmin batun da daukacin masanan da suka hallarci taron na Bonn suka yi amanna da shi, shine cewa akwai alamu masu ƙarfi waɗanda ke nuni da cewa za'a iya cimma yarjejeniya zuwa ranar 2 ga watan Augusta. Sai dai abinda masanan bassu so yin hasashe akai ba shine yadda yarjejeniyar za ta ɗore, abin da wani masani Doughlas Johnson wanda ya wallafa littafai da dama akan Sudan da Sudan ta Kudu wanda kuma ya shafe shekaru 40 yana aiki a yankin ya yi tababa kenan akai. A cewarsa a can baya wa'adi na diplomasiyya a Sudan da aka yi ta sanyawa ya haifar da wasu yan sakamako
"Ya samar da ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniya a takarda da kuma cewa tsare-tsaren yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar zai zo daga baya. A takaice dai ba wata yarjejeniya ce mai ƙwari ba kuma a halin da ake ciki yanzu ban ga wani ƙudiri a yadda yanayin siyasar cikin gida ke tafiya a Sudan da kuma siyasar dake tsakanin ƙasashen biyu cewa za'a sanya wa'adi zai kai ga samar da yarjejeniya akan waɗannan muhimman batutuwa ba.
Tattaunawa da shawarwari ta daɗe tana gudana tsakanin ɓangarorin biyu tun ma kafin Sudan ta kudu ta sami 'yancin kai a watan Yulin bara. Ɗauki misali rabon arzikin mai, Sudan ta bukaci a biya ta kuɗi mai yawa saboda ratsawa da bututun man ta cikin ƙasarta, bayan kiki-kaka na tsawon lokaci Sudan ta kudu ta yarda ta yi kari kudin fiton zuwa Dala tara na Amirka. Hakanan kuma gwamnatin ta gabatar da shirin kuri'ar raba gardama akan yankin Abyei mai arzikin mai wanda ƙasashen biyu kowace ke da'awar mallakinta ne. A waje guda dai martanin Sudan ta arewa na nuna halin ko in kula. Khalid Musa Dafalla shine mukaddashin jakadan Sudan a nan Jamus.
" Jigilar man Sudan ta Kudu ta cikin ƙasar Sudan na buƙatar a warware matsalar tsaro tukunna, ba za mu amince mu bada haɗin kai akan arzikin mai ba, alhali a waje guda suna ɗaurewa yan tawaye gindi suna basu makamai, kuma ba'a sulhunta matsalolin tsaro ba..
A hukumance dai Juba fadar gwamnatin Sudan ta Kudu ta musanta zargin taimakawa yan tawaye, sai dai akwai alamun bada dan taimako ƙalilan kasancewar yan tawaye dake yankin Blue Nile dana Kudancin Kordofan sun taɓa zama reshe na ƙungiyar yan tawayen SPLM, kuma SPLM din ce a yanzu take kokarin kafa gwamnati a Juba. A saboda haka taron masanan na Bonn yace zai yi wuya matuka Juba ta daina taimakawa tsoffin aminan da suka taimaka musu a filin daga ta hanyar saka musu da musayar mai.
A hannu guda dai yayin da yan siyasa suke cigaba da jayayya, su kuwa jama'ar dake zaune a kan iyaka basu da wata matsala sosai da juna. A mafi akasarin wurare babu rigima tsakanin al'umar wannan yanki da tawarorinsu dake daya tsallaken. Luka Biong Deng Kuong tsohon minista ne a gwamnatin Sudan ta Kudu: A yanzu kuma yana gudanar da wata ƙungiya mai zaman kanta wadda ke taimakawa al'umomin dake zaune kusa da kan iyaka.
" Akwai wasu yan arewacin Sudan waɗanda kan yi kasadar shigar da kayan sayarwa zuwa Kudu. Halin dai da ake ciki ya banbanta mutane suna kokarin gudanar da rayuwarsu yadda suka saba da yin mu'amala da sauran jama'a.
Duk da matsaloli akwai haske na wanzuwar rayuwa ga mazauna kan iyaka. Akalla babu alamar rayuwarsu za ta tabarbare. Masana sun yi itifakin cewa ɓangarorin biyu basu da niyyar gwabza yaƙi a nan kurkusa.
Mawallafa: Daniel Patrick Pelz/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Zainab Mohammed Abubakar