Najeriya: Ko talaka zai mori dokar haraji?
December 18, 2025
Sabuwar takaddama ce ta kuno kai kan batun sabuwar dokar harajin da gwamnatin Najeriyar ta tsara za ta fara aiwatar da ita, a farkon shekara mai zuwa ta 2026. Gamayyar jamiyyun adawar sun bayyana damuwa a kan halin da al'ummar kasar ke ciki na koma-bayan tattalin arziki, inda suke ganin ba wannan ne lokacin da ya dace a sake kara dora musu wani nauyi ba.
Kama daga Peter Obi na jam'iyyar Labour da Atiku Abubakar da ma David Mark na jam'iyyar ADC da sauran jam'iyyun adawar Najeriyar ne dai, suka nuna cewa a sake sabon lale. To sai dai tanade-tanaden da aka yi a kan dokar harajin ta Najeriyar, ya samar da tsare-tsaren wadanda za su biya harajin. Daga wanda yake samun albashi ko kudin shigar da suka kai Naira miliyan biyu da 200,000 da zai biya kashi 15 cikin 100 kowane wata, har zuwa wanda zai biya kashi 25 cikin 100 idan yana samun Naira milyan 25.
'Yan Najeriya da dama na nuna damuwa a kan halin da za su shiga, abin da ya sanya kungiyoyin farar hula shiga cikin batun harajin a Najeriya. A yayin da wannan ke faruwa, dan majalisar wakilan Najeriyar Abdussammad Dasuki ya ce, dokar da aka wallafa ta bambanta da wacce suka amince da ita, batun da a yanzu ke tayar da kura a yanayi na allura na neman tono garma.