1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Wacce tafi kowa shekaru a duniya ta rasu a Spain

August 20, 2024

Wacce ta fi kowa shekaru a duniya kuma ta shaida yakin duniya na daya da na biyu Maria Branyas Morera, 'yar shekara 117 ta mutu a kasar Spain, bayan shafe shekaru a gidan kula da tsofaffi.

Maria Branyas Morera a bikin cikarta shekaru 117 da haihuwa
Maria Branyas Morera a bikin cikarta shekaru 117 da haihuwa Hoto: Wikipedia/Familienarchiv Branyas Morera

Iyalanta sun ce Branyas ta shafe shekaru 20 a gidan kula da tsofaffi na Santa Maria del Tura da ke shiyyar arewa maso gabashin Spain, kafin jikinta ya tabarbare a 'yan makonnin da suka gabata, kamar yadda suka sanar a shafin X.

Karin bayani: Fatima al-Fihri: Wace ta gina jami'a mafi tsufa a duniya

Kundin adana bayanan tarihi da kuma ayyana gagarumar bajinta na duniya na Guinness World Records, ya sanar da Branyas a matsayin wacce ta fi kowa shekaru a duniya bayan mutuwar mai rike da kambun 'yar kasar Faransa Lucile Randon mai shekaru 118 da ta mutu a 2023.

Karin bayani: Dan-wasa mafi tsufa a gasar kofin Duniya

Kwararrun likitocin da suka yi bincike kan kwayoyin halittunta na Jami'ar Barcelona sun yi matukar mamakin yadda dattijuwar ke iya bada labarin abin da ya faru a lokacin da take shekaru 4 a duniya.