1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aminata Toure: Bajamushiya bakar fata

June 1, 2021

Aminata Touré ta kasance sananniya a Jamus, matsayin Bajamushiya bakar fata ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban majalisa. Mai shekaru 28 a duniya, na shirin fadada siyasarta zuwa birnin Berlin.

Aminata Toure  Vize-Präsidentin Landtag Schleswig Holstein
Aminata Touré Bajamushiyar bakar fata, kana fitacciyar 'yar siyasa a JamusHoto: Miodrag Soric/DW

Aminata Toure ta kasance matashiyar Bajamushiya bakar fata da ta samu tagomashi cikin harkokin siyasar Jamus. 'Yar fafuka kuma 'yar siyasa matashiyar mai shekaru 28 a duniya, ta kasance 'yar jami'iyyar masu fafutukar kare muhalli ta "The Greens." Aminata na shirin shiga takara a majalisar wakilan tarayya ta Bundestag. Shekaru biyu kena da wannan matashiya ta bayyana a fagen siyasar Jamus. Ta kasance irin 'yan siyasar nan da abubuwa ba su cika rikita su ba, ko da kuwa ba a san me zai biyo baya ba.

Rashin tsoro da fargaba

Misali shi ne, lokacin da wasu masu zanga-zanga suka je kofar majalisar Kiel, suna neman matsugunai ga irin mata da yara  da ke fuskantar matsalar cin zarafi. Cikin nutsuwa Aminata ta saurari matsalolinsu da kuma abun da suke muradi.

Aminata Toure na tunkarar matsaloli kai tsayeHoto: Miodrag Soric/DW

Nan take ta yi jawabin martani, inda ta soki manufofin gwamnatin jihar Kiel, gwamnatin da har jam'iyyarta ta kare muhalli ke ciki. Ta daukar wa masu zanga-zangar alkawarinn taimaka wa. Nan take suka watse cikin murna da farin ciki. Aminata ta ce: "Na kasance cikin mutanen wannan karni da ke cewa tsawon shekaru ba a yarda da mu a matsayin bangare na wannan al'umma ba, duk da cewar muma muna da rawar takawa. Akwai abubuwan da muke la'anta. Amma kuma muna da shawarwari kan yadda abubuwa za su inganta."

Damuwa da yanayin 'yan ci-rani

Aminata dai ta kasance mai fafutukar kare 'yancin mata musamman matasa 'yan ci-rani. Tana yaki da nuna wariyar launin fata. Tana da ra'ayi kan tsarin ilimi da kuma batutuwa da suka shafi shige da ficen kasa. A cewarta, idan mutane suka mutu cikin Tekun Bahr Rum a kokarinsu na tsalleka wa zuwa Turai, wajibi ne abun ya dami wadanda ke nan, ba wai wadanda ke Afirka kadai ba: "Tabbas hakan ba zai sa in ki nuna damuwa ba, bisa la'akari da daruruwan mutanen da suka mutu ko kuma suka nutse a cikin Tekun Bahar Rum, ko kuma yadda ake wasan siyasa da mutanen da suka fito daga yammacin Sahara ba. Idan ka kalli halin da ake ciki a Misar da Spain da irin labaran da ake ji, tabbas hakan abun damuwa ne, kuma ya kamata ya shafi har wanda ba shi da wata alaka da nahiyar Afirka."
Shekaru biyun da suka gabata ne dai tashar DW ta tattauna da matashiyar 'yar siyasar, wadda da ganinta ka san ba ta fargabar komai, saboda a kullum ta na hanyar balaguro. Tsarin ilimi, musamman bangaren tarihin mulkin mallaka na da muhimmanci ga Aminata. Ta na ganin a nan Jamus alal misali, yara 'yan makaranta ba su da masaniya dangane da miyagun abubuwan da Turawan mulkin mallaka suka tabka a Afirka, kafin yakin duniya na daya.

Batun ilimi ne daya daga cikin abubuwan da matashiyar 'yar siyasar ta damu da shiHoto: DW/M.Soric

Matsalolin mulkin mallaka

Aminata na da muradin sauyi a wannan bangare: "Muna son a sanya nazarin mulkin mallaka sosai a cikin jadawalin karatu a makarantu, don hakan zai ba mu damar fahimtar wariyar da ke faruwa a yau. Musamman lokacin da muke magana kan wariyar launin fata kan bakar fata. Wacce irin rawa hotunan zamanin mulkin mallaka suka taka a cikin karni na 19, wanda ke da tasiri har zuwa yau? Kuma wannan shi ne dalilin da ya sa wadannan abubuwa ke taka rawa a nan Schleswig-Holstein."

Sai dai gwagwarmayarta ta siyasa na samun martani na suka, musamman a shafukan sada zumunta. Amma duk da haka a kullum tana samun karin masoya da masu yi mata fatan alkairi, kuma matasa da ke da ra'ayin shiga siyasa a nan Jamus, kan nemi shawarwarin Aminata Toure.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani