Adadin wadanda suka mutu a jihar Filaton Najeriya na karuwa
December 27, 2023Adadin wadanda suka mutu a jerin hare-haren da 'yan bindiga suka kaddamar a kan wasu kayukan jihar Filato a Najeriya a karshen mako, ya kai kusan mutum 200 a halin yanzu.
Hare-hare ne da suka faro daga yankin karamar hukumar Bokkos da yammacin ranar Lahadi, inda kuma ya dangana da karamar hukumar Barikin Ladi.
Jagoran karamar hukumar Bokkos, Monday Kassah ya ce mutane 148 ne aka kashe a lamarin jimilla, yayin da Dickson Challom wani zababben dan majalisa daga yankin Barikin Ladi, ya tabbatar da cewa maharan sun kashe mutane 50.
Akwai ma wasu daruruwan mutanen da 'yan bindigar suka jikkata a hare-haren a cewar mahukunta.
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International dai ta zargi gwamnatin Najeriya da rashin daukar matakan da za su kawo karshen kare-kashe da ake yi a yankunan karkara a jihar Filato.