Shin taron Davos zai magance rikice-rikicen duniya?
January 20, 2026
An fara taron shekara-shekara na tattalin arzikin duniya a birnin Davos na kasar Switzerland karo na 56. Kusan mutane 3,000 ne ke halartar taron ciki har da shugabannin kasashe da na gwamnatoci har da shugabannin kungiyoyin farar hula. Wannan taro da ke hada kan manyan kasashen duniya kan tattaalin arziki, ya zo ne a daidai lokacin da duniya ke cikin yanayin tashin hankali na rarrabuwan kawuna a fannin siyasa da tattalin arziki da sauyin fasaha da ake gani cikin hanzari.
Karin bayani: Amurka da EU sun cimma yarjejeniyar kasuwanci
Barazanar Trump na labta wa kungiyar Tarayyar Turai haraji saboda adawa da matakinsa na kwace yankin Greenland daga hannun kasar Denmark na zama babban abin da ke daukar hankali. Shugabar Hukumar Zartaswa ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce lokaci ya yi da EU za ta gina sabuwar Turai mai cin gashin kanta.
"Wannan sauyi da ke girgiza siyasar duniya, dole ta zama izina ga Turai. Kuma a ganina, sauyin da muke ciki a yau wata dama ce a hakikanin gaskiya don gina sabon salo na 'yancin kai na Turai." in ji babbar jami'ar ta Kungiyar Tarayyar Turai
Wace rawa Trump zai taka a Davos?
Shugaban Amurka Donald Trump zai gabatar da jawabi a tsakiyar mako kan siyasa da kasuwanci. Amma tuni 'yan gwagwarmaya suka ja daga na zazzafar zanga-zangar adawa da manufofinsa. Ita kuwa China wacce ke cikin manyan kasashen da ke daukar hankali, ta caccaki matakin da wasu kasashe ke dauka na fatali da dokokin kasa da kasa musamman na kasuwanci,
Beijing na gugar zana ne da Washington a fakaice, kamar yadda mataimakin shugaban kasar He Lifeng ke cewa: "Dole mu yi tsayin daka wajen tabbatar da ra'ayin bangarori daban-daban da kuma inganta tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa mai adalci. Ana ganin kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba. Ayyukan bai-daya da yarjejeniyoyin kasuwanci na wasu kasashe sun saba wa ka'idojin Kungiyar Cinikayya ta Duniya."
Rikicin Ukraine da Rasha na daukar hankali
Ana kayautata zaton taron Davos zai zama dandalin samun ci gaba na kawo karshen yakin Ukraine da Rasha, bayan da kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya tabbatar da cewa wakilin Rasha za su gana da na Amurka a birnin Davos.
Karin bayani: Davos: Kalubalen fasahar kirkira ta AI a duniya mai sarkakiya
Tasirin fasahar kirkirarriyar basira ta AI, jigo ne a taron. Shugabannin kamfanoni na gargadin wasu ma'aikatu da ke shirin amfana da AI, sun kasa samun nasara saboda rashin isasshen shiri. Sai dai shugabannin taron, na nazari kan tasirin AI, yyin da kamfaanoni irin su Microsopft da Amazon ke muhawara kan barazanar AI wajen kutsen bayanai, wanda ake ganin zai rage tasirin karbuwar fasahar.