1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Wakilan Isra'ila da Hamas zasu yi ganawar keke da keke

October 5, 2025

Majiyoyin Isra'ila sun ce akwai fursunonin yakin kasar 48 da ke hannun Hamas da kuma ake hasashen cewa ashirin na raye.

Wasu daga cikin gine-ginen da Isra'ila ta tarwatsa a Gaza
Wasu daga cikin gine-ginen da Isra'ila ta tarwatsa a GazaHoto: Khames Alrefi/Anadolu Agency/IMAGO

Masar dai ta gayyaci wakilan Isra'ila da na kungiyar Hamas tattaunawa domin tsara jadawalin musayar fursunoni yaki tsakanin bangarorin biyu, bayan daftarin wanzar da zaman lafiya da tsagaita bude wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar.

Karin bayani: Qatar da Masar na jiran ra'ayin Isra'ila kan yakin Gaza

Kafofin yada labaran Masar sun rawaito cewa ana sa ran gudanar da taron a birnin al-Arish da ke gabar Tsibirin Sinai da Sharm El-Sheikh na kusa da yankin Zirin Gaza. Ana sa ran Manzon Amurka na Musamman a yankin Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff zai halarci taron.

Karin bayani:An gaza sasanta Isra'ila da Hamas a Qatar 

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yana da yakinin cewa nan bada jimawa ba za a saki dukkan fursunonin yakin kasar da ke hannun kungiyar Hamas a yankin Gaza, wanda kuma hakan babbar nasara ce ga hukumomin Tel Aviv.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW