1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

'Yar Ghana ta yi fice a wakokin zamani

April 28, 2021

Wakokin gambara da aka fi sani da Rap Music a Turance su ne a yanzu haka ke tashe a tsakankanin matasa a kasar Ghana, sai dai ba kasafai ake samun mata masu wakokin na Rap ba.

DW GirlZOffMute, Ghana | Chelsea Boakye, DW & Samera Buari, Rapperin
Hoto: Isaac Kaledzi/DW

Wakokin gambara da aka fi sani da Rap Music a Turance sune a yanzu haka ke tasahe a tsakankanin matasa a kasar Ghana, sai dai ba kasafai ake samun mata masu wakokin na Rap ba. Samera Buari wata matshiya ce kwaya daya tilo a birnin Accra da ta rungumi wakar ta gambara a matsayin sana'a.

Samera Buari da aka fi sani da Esbee 'yar shekaru 27 da haihuwa da ta kwashe shekaru sama da goma ta na waka, da fari dai ta fara waka cikin abokananta  mata da suka kafa wata kungiyar mawaka mata mai suna 3D. Kimani 'yan shekaru kalilan ke nan da Samera Buari ta balle daga wannan kungiyar domin cin gashin kanta, inda ta mayar da hankali wajen wakokin gambara na Rap, amma ta ce ba abu ba ne mai sauki.

Duk da wahalhalun da kalubalen da ta fuskanta, Esbee ba ta karaya ba yanzu haka ma tana kan aiki a wata sabuwar wakar rap din da take son fitar wa. Wakokin na wannan matashiyar na matukar zaburar da matasa maza da mata tare da kallon ta a matsayin hanyar rufa wa kai asiri. Babban abin da ya rage ga  wannan matashiya shi ne aiki tukuru domin ganin hakarta ta cimma ruwa.