Ina Hisbollah da sauran kawayen Iran?
June 23, 2025
Shiru da bakinta da rashin daukan matsayi da Hezbollah ta yi tun bayan fara fada tsakanin Isra'ila da Iran, ya sa ana dasa ayar tambaya kan inda Kawayen gwamnatin Tehran suka shiga, kama daga 'yan Houthi har i zuwa 'yan Shi'an Iraqi.
Karin bayani: Amurka na son China ta hana Iran toshe mashigin ruwan Hormuz
A cikin 'yan shekarun baya bayan nan dai, ba kasafai Iran ke shiga cikin rikici ita kadai ba. Hasali ma, a karkashin taimakon kudade masu yawa da samar da makamai da kuma ba da horon soji, fadar mulki ta Tehran ta samar da ma'amala mai karfi da abokan kawancenta na Shi'a a yankin, wadanda ke taimaka wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen yakar Isra'ila. Ko da Ronnie Chatah, mai sharhi kan lamuran siyasa, sai da ya ce tasirin da Iran ke da shi ba ya rasa nasaba da kusanci da take da shi da 'yan Shi'a.
Mayakan Hezbollah na Lebanon da 'yan Houthi na Yemen da Hamas na Gaza da 'yan Shi'a na Iraki sun kasance masu goyon bayan gwamnatin Tehran. Haka shi ma Bashar al-Assad, wanda ya mulki kasar Syria, ya dade yana jan ragamar mulki ne bisa taimakon kasar Iran.
Amma dai a 'yan watannin da suka gabata, jerin magoya bayan Iran sun durkushe daya bayan daya, saboda matakin soji da firaministan Isra'ila Netanyahu ya dauka a kansu da kuma manufar sauyin fuska a yankin Gabas ta Tsakiya da ya sa a gaba. Alal hakika, Hamas ta raunana sakamakon yakin Gaza, kuma an kashe muhimman shugabanni irin su Ismail Haniyeh da Yahaya Sinwar. Su kuwa 'yan Houthi a Yeman na shan suka sakamakon hare-haren da suke kai wa Isra'ila.
Karin bayani: Ana ci gaba da fito na fito tsakanin Iran da Isra'ila
Sannan masu kishin Islama sun hambarar da gwamnatin Assad na Syria, kuma Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai kan cibiyoyin soji. Kuma kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta sha kakkausar suka a yakin da suka yi da Isra'ila a karshen shekarar da ta gabata, a cewar masanin kimiyyar siyasa Mustafa Kamel as-sayd na jami'ar Alkahira:
"Hezbollah ta yi rauni sosai, an kashe shugabanninta. Wannan ya sa mayakanta sun janye daga kudancin kasar, kuma har yanzu Isra'ila na kai hare-hare."
A rikicin da ake fama da shi tsakanin Isra'ila da Iran, kungiyar Hezbollah ba ce uffan kan abin da ke wakana ba. Amma wai shin, Hezbollah ba ta zarafin taimaka wa Iran ne ko kuma ba ta da karfin tsaro ne? Dan jarida na kasar Lebanon Amin Qamouriyeh, ya ce har yanzu kungiyar Hezbollah a shirye take ta shiga yaki, inda ya danganta shirin kungiyar da dabarar yaki.
Karin bayani:Iran ta sha alwashin kare kanta "ta ko halin kaka"
"Hezbullah na ganin cewa a halin yanzu Iran na da karfin kare kanta. Har yanzu ba a kai ga rugujewar gwamnatin Iran ba. Har zuwa wannan lokacin, Hezbullah na ci gaba da taka-tsantsan."
Sai dai, a yayin da Hezbollah ke shakkar shiga yaki, su kuwa 'yan Houthi na Yemen a shirye suke su shiga yaki. A halin yanzu, da alama Iran ba ta da sha'awar hada kai da 'yan barandanta a yankin wajen kalubalantar Isra'ila. Sannan, wadannan kawayen Iran na da nasu muradi, saboda haka ba su da niyyar karbar umarni, a cewar Mustafa Kamel as-Sayyed na Jami’ar Alkahira:
"Ina kokwanto kan cewar batun karbar umarni ne kawai daga Tehran. Duk wadannan kungiyoyi suna suna cin gashin kansu ne kuma suna fuskantar matsin lamba a kasashensu."
Kasashen Lebanon da Iraki sun bukaci a nesanta su daga daga rikicin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila a halin yanzu. Dama, Iran ta gina manyan cibiyoyi a Iraki tare da neman yin tasiri a kan mayakan Shi'a da dama. Saboda haka, hare-hare kan sojojin Amurka zai sanya matsin lamba ga Trump, kuma da alama Iran na son kauce wa wannan mataki.