Nadin sabon shugaban hukumar zaben Najeriya
October 22, 2015Farfesa Mahmood Yakubu ya fara karatunsa na boko ne a jihar ta Bauchi kafin yaje jami'ar Usman dan Fodio da ke Sokoto inda ya karanta tarihi a digirinsa na farko kuma ya kafa tarihin da babu irinsa a daukacin Arewacin kasar har ya zuwa yanzu. A shekarar 1991 ne dai Yakubu ya samu digirinsa na digirgir a jami'ar Oxford ta kasar Ingila yana da shekaru 29, inda kuma ya samu kyaututtuka daban-daban saboda hazakarsa. Sabon shugaban hukumar ta INEC ya yi koyarwa a jami'oi da suka hadar da Ahmadu Bello da ke Zaria da kuma jami'ar Jos , kafin daga baya a shekara ta 2007 ya shugabanci gidauniyar tallafawa makarantun gaba da sakandare ta kasar har na tsawon wasu shekaru biyar.
Kwararre a fannin tarihi da tsaro
Farfesa Yakubu dai na da mace guda da 'ya'ya Hudu. Kuma kwararre ne ga siyasar tarihi da kuma yakin sunkuru da na ta'addanci a karance. Duk da cewar dai Farfesa yakubu yaki yarda ya ambaci wani abu game da shi kansa har sai bayan ya fuskanci tacewar majalisar dattawan kasar da kuma ganewa idanunsa abin da sabon offishin nasa ya kunsa. To sai dai kuma mafi yawan mutanen da suka yi hulda da shi sun baiyana shi a matsayin mai hazaka da dagewar da ta kai shi ga jagorantar gidauniyar da ke zaman daya mafiya yawan kudi a cikinta ba kuma tare da fuskantar wani zargin almundahana ba. Dr. Garba Umar Kyari na zaman daya daga cikin wadanda a baya suka yi hulda da sabon shugaban a matakai daban- daban, ya kuma ce mutum ne mai hazaka kwarai da gaske kuma ya yi rawar gani sosai a mukaman da ya rike a baya.
Hazaka da jajircewa a aiki
Hazakar ta Mahmood Yakubu dai daga dukkan alamu na zaman babban jarin da ya dauki hankalin 'ya'yan majalisar kasar da suka zauna suka amince da nadin nasa domin aiki mafi tasiri na alkalancin zabe cikin kasar ta Najeriya a fadar Aminu Waziri Tambuwal da ke zaman gwamnan jihar Sokoto da kuma ya bayyana nadin nasa tun da farkon fari. To sai dai kuma masu nazarin harkokin siyasar kasar ta Najeriya na kallon ya wuce hazaka da sanin ya kamata a matsayin na kan gaba a cikin abun da ake bukatar gani ga magajin Farfesa Attahiru Muhammad Jega mutumin da ya dauki INEC daga hukumar da tai kaurin suna na gazawa cikin kasar ya mai da ita mafi kima a idanu na 'yan kasar dama bakinta. Abin kuma da a cewar Dr Yunusa tanko da ke zaman shugaban hukumar NCP kuma tsohon shugaban kwamitin hadin gwiwar jam'iyyun kasar a zaben da ya shude, sabon shugaban na bukatar kallon tsaf da kuma sauraron kowa a kan hanyarsa ta dorawa da ma kila cimma sa'a a jan aikin da ke gabansa a yanzu. Babban aikin da ke gaban sabon shugaban hukumar ta INEC dai daga dukkan alamu na zaman dorawa daga shirin mayar da tsarin zaben kasar irin na zamani domin kaucewa magudin da ke zaman al'ada can baya.