1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wanene ya ƙirƙiro ƙungiyar nan ta kare muhalli mai suna “Greenpeace Inte...

Bashir, AbbaMay 27, 2008

Taƙaitaccen tarihin mutumin da ya ƙirƙiro ƙungiyar kare muhalli mai suna “Greenpeace International”

Taron ƙasashen duniya akan kare muhalli, a birnin Buenos Aires, na ƙasar ArgentinaHoto: AP

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga Hannun Malama Harira Abdullahi daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijer. Malamar cewa ta yi, wai shin, wanene ya ƙirƙiro ƙungiyar nan mai suna “Greenpeace International”, wato ƙungiyar kare muhalli ta ƙasa da ƙasa?


Amsa: To ƙashin bayan kafa wannan ƙungiya shi ne Dr. Patrick Moore, duk da cewa a yanzu yana sukan al'amarin ƙungiyar. Yana da takardar shaida ta digiri na matsayin Dr., wanda ya samu daga cibiyar dake koyar da mu'amalar dake tsakanin tsirrai, dabbobi da jama'a,  da kuma muhallin da suke ciki, wadda ya samu a jami'ar ƙasar Columbia.


Da farko dai, ita wannan ƙungiya, ta fara ne a matsayin wata ƙungiya mai sukar al'amarin gwamnatin  Amurka akan abin da ya  shafi ƙera makaman nukiliya, kafin ta rikiɗe ta zama ƙungiya ta ƙasa da ƙasa mai da'awar kula da kuma kare muhalli.


DR. Patrick Moore ya yi suna a duniya akan harkokin da suka shafi tsirrai, dabbobi da kuma muhalli. Ya fara wannan harka ne daga zama ɗan gwagwarmaya a ƙungiyar kare muhallin ta ƙasa da ƙasa, kafin kuma ya mai da hankalinsa akan ƙoƙarin gamayya na gano hanyar warware matsalolin da muhalli ke ciki.


Yana ba da jawabai da kuma yin bita akai-akai a jami'o'i da manyan taruka. A matsayin sa na wanda ya yi fice da kuma zama babban mai magana da yawun wata ƙungiya mai suna “Forest Alliance”, yana fitowa a gidajen talabijin da rediyo da kuma jaridu.


Har ila yau, a matsayinsa na Darakta kuma mataimakin shugaban  ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta muhalli da harkokin gwamnati akan ruwa daga 1995-1998, ya yi aiki tuƙuru don wayar da kai akan ribar dake tattare da fasaha akan sake amfani da ƙasa. Cikakken marubuci ne kuma mai ɗaukar hoto, wanda kwanan nan ya buga wani littafi mai suna “Green Spirit—Trees Are the answer”, wato littafi ne akan gandun daji da muhalli, mai taken dashen itatuwa shi ne tushen kare muhalli. DR. Moore ya yi amanna da cewa hanya ɗaya tilo da za a bi don warware rigingimun da suka shafi muhalli, yanayin rayuwa da al'amuran tattalin arziki, ita ce ta tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma yarda akan matsayi ɗaya da aka ɗauka.


A 1991 ne Dr.Moore ya kafa wata ƙungiya mai suna “Greenspirit”. Ita dai ƙungiyar tana ba da shawarwari ne akan abubuwan da suka shafi manufofi akan muhalli da albarkatun ƙasa, makamashi da kuma canjin yanayi.