Wani Ba' amirke zai fuskanci shari'a Koriya ta Arewa
April 27, 2013Talla
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa tsakanin kasashen biyu. Ba'amirken dan shekaru 44 amma mai asali daga Koriyar za a kai shi kotu domin ya amsa tambayoyi akan zargen da ake masa na cewa ya yi yukunkurin kifar da gwamnatin kasar mai bin tsarin kominisanci. Pae Jun Ho zai fuskanci hukuncin kisa in har ya amsa laifin aikata hakan. A watan Nuwamban bara ne aka kame wannan mutun a lokacin da ya je kasar tare da wasu 'yan yawon bude ido.. A dai 'yan shekarun da suka gabata an ta kame 'yan kasar Amirka a Koriya ta Arewa, To amma sai aka sake su bayan da Amirkan ta tura wani manzo na musamman.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman