Wani soron beni ya ruguje a Kenya
April 30, 2016Talla
A cewar ma'aikatan agaji na Red Cross na kasar ta Kenya kimanin wasu mutane 150 sun samu mafaka a wani kauye da ke yankin da wannan hadari ya faru. Kuma kawo yanzu an samu ceto mutane kusan 60 cikin su har da wani jariri, amma kuma majiyar ta ce akwai mutane da dama karkashin baraguzan ginin. Soron benin dai ya ruguje ne da wajejen karfe tara da rabi na dare agogon kasar a wata unguwa mai cinkoson jama'a ta Huruma da ke arewa maso gabashin birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar.