1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Wani dan Afghanistan ya kashe mutane biyu a kudancin Jamus

January 22, 2025

Hukumomin yankin sun cafke matashin da ake zargi da kai harin da wuka, duk da cewa ba su bayyana makasudin kai farmakin ba. Harin ka iya shafar zaben da za a gudanar a Jamus da jam'iyyar AfD mai kyamar baki ke tasiri.

Wurin da aka kai harin a birnin Aschaffenburg na jihar Bavaria da ke kudancin Jamus
Wurin da aka kai harin a birnin Aschaffenburg na jihar Bavaria da ke kudancin JamusHoto: Ralf Hettler/dpa/picture alliance

Wani 'dan asalin Afghanistan da ke zaune a nan Jamus ya far wa wasu mutane da wuka inda ya halaka mutum biyu ciki har da yaro karami 'dan shekara biyu a birnin Aschaffenburg da ke jihar Bavaria. 'Yan sandan yankin sun ce maharin ya jikkata wasu mutanen guda biyu inda suke ci gaba da karbar magani a asibiti.

Karin bayani:Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus? 

'Yan sandan Bavaria sun cafke mutumin da ake zargi da kai harin, lamarin na daya daga cikin barazanar da Jamus take fuskanta na kai hare-haren kan mai uwa da wabi da wuka a watannin baya bayan nan. Hukumomin tsaron yankin da ke kudancin Jamus na ci gaba da bincike kan harin duk da cewa ba su bayyana makasudin kai farmakin ba.

Karin bayani: Ana bincike kan barazanar sake kai hari a Jamus

Harin na zuwa ne gabanin zaben wuri da za a gudanar a Jamus a ranar 23 ga watan Fabrairu, inda kawancen jam'iyyun CDU/CSU ke kan gaba da kashi 30 cikin 100 a kuri'ar jin ra'ayin mutane da aka gudanar, yayin da jam'iyyar AfD mai ra'yin kyamar baki ke bi mata da kashi 20, sai kuma jam'iyyar SPD ta shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ke a matsayi na uku.