Wani dan bindiga ya bude wuta kan dalibai a Minneapolis
August 27, 2025
Dan bindiga ya bude wuta kan daliban da ke karatu a wata makaranta da ke majami'ar Minneapolis na Amurka, inda ya halaka yara biyu tare da jikkata wasu 17.
karin bayani:An kashe mutane a gidan tarihin Yahudawa a Washington
Baturen 'yan sandan Minneapolis Brian O'Hara, ya shaida wa manema labarai cewa maharin ya bude wuta ne kan yaran a daidai lokacin da suke gangamin makon dawo wa makaranta. Maharin ya yi amfani da bindiga wajen harbin kan mai uwa da wabi. Wasu hotuna da aka yada a kafafen sada zumunta sun nuna yadda iyaye suka yi ta tururuwa zuwa makarantar domin kubutar da 'yayansu.
karin bayani:Rushdie zai kaddamar da sabon littafi tun bayan kai masa hari
Gwamnan Minnesota Tim Walz, ya wallafa sakon ta'aziyya a shafinsa na X ga iyalai da malaman makarantar da aka kai wa mummunar farmaki.