Wani dan bindiga ya kashe mutane a Amurka
May 7, 2023
Talla
Wani dan bindiga dadi ya bude wuta a kan jama'a a birnin Allen na jihar Texas da ke Amurka, inda bayanai ke tabbatar da cewa ya yi sanadin mutuwar akalla mutane tara.
Dan bindigar wanda ya bude wutar a wani rukunin shaguna da ke dauke da mutane da dama da ke cefanen karshen mako, ya kuma jikkata karin wadanda tsautsayi ya rutsa da su.
'Yan sanda a birnin na Allen dai sun ce maharin wanda ya isa cikin wata karamar mota, an yi nasarar halaka shi jim kadan bayan aikata wannan danyen aiki.
Hukumomin ba su kaiga samar da bayyanai a kan sa ba, sai dai sun tabbatar da kasancewarsa guda daga cikin gawarwakin da aka kwashe a wajen.
Daga cikin wadanda ya kashe har da wasu kananan yara wadanda shekarunsu ba su wuce biyar ba.