1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Wani dan bindiga ya kashe mutane biyar a Croatia

Zainab Mohammed Abubakar
July 22, 2024

Harin da aka kai a garin Daruvar, ya kuma raunata mutane da yawa, a wani lamari da ba kasafai ake ganin irinsa ba a kasar ta Balkan, a cewar kafofin yada labaran Croatia.

DaruvarHoto: NIKOLA BLAZEKOVIC/AFP

Kafar yada labarai ta HRT ta ce dan bindiga da ba a san ko wane ne ba, ya shiga wani gidan kula da tsofaffi da ke garin Daruvar, mai tazarar kilomita 130 daga gabashin Zagreb, ya fara harbi.

Akalla mutane biyar ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harbin. Majiyar ta ce wanda ake zargin ya gudu amma daga baya ‘yan sanda suka kama shi.

Croatia ta yi yakin neman 'yancin kai a lokacin ballewar Yugoslavia daga 1991 zuwa 1995. A bara a makwabciyarta Serbia, ta fuskanci hare-haren wuce gona da iri, ciki har da kisan kiyashi a wata makaranta da ke babban birnin Belgrade inda mutane 10 suka mutu.