Wani hari a gabashin Jamhuriyar Nijar ya hallaka mutane uku
August 28, 2015Talla
Wannan harin ya wakana ne tun a farkon wannan mako amma kuma sai a yammacin jiya Alhamis aka samu labarin daga wata majiya ta jami'an tsaron kasar. A kalla dai 'yan gudun hijira dubu 150 ne da suka guje wa yakin da ake da Boko Haram daga Najeriya, ke a yankin Jihar Diffa, inda gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta saka dokar ta-baci, tare kuma da kame mutanen da ake zarki da alaka da 'yan kungiyar ta Boko Haram da yawansu ya kai mutune 1.100 kawo yanzu.