1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani hari ya salwantar da rayuka a Kabul

Mouhamadou Awal Balarabe
December 22, 2020

Akalla mutane biyar sun mutu ciki har da likitoci 4, a wani harin kunar bakin wake da aka a Kabul babban birnin Afghanistan. Babu wanda ya dauki alhakkin harin, amma ya yi kama da wanda 'yan Taliban ke kaiwa.

Afghanistan Kabul Bombenanschlag
Hoto: Rahmat Gul/AP/picture alliance

'Yan sanda a Afghanistan sun ce akalla mutane biyar ciki har da likitoci hudu da ke aiki a wani gidan yari da ake tsare da 'yan kungiyar Taliban sun rasa rayukansu a Kabul, a lokacin da wani bam ya fashe a karkashin motarsu. Wannan dai shi ne hari na biyu mafi muni da aka kai cikin kwanaki biyun da suka gabata a babban birnin na Afghanistan, inda a ranar Lahadin da ta gabata, mutane 10 mutu yayin da kusan 50 suka jikkata a sakamakon fashewar wani bam da ke cikin wata mota.


A ‘yan watannin da suka gabata dai, babban birnin Afghanistan ya yi fama da rikice-rikice duk da tattaunawar zaman lafiya da ake yi tsakanin‘ yan Taliban da gwamnati tun watan Satumba a Doha. Sai dai Kungiyar IS ta dauki alhakin hare-hare da zubar da jini na watanni baya-bayannan a babban birnin kasar ta Afghanistan, ciki har da wadanda aka kai a jami'a da kuma wata cibiyar ilimi, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 50.