Harin 'yan bindiga ya hallaka mutane da yawa a Sinai
July 1, 2015Talla
Akalla sojoji 15 da kuma 'yan tarzoma da yawa sun rasu a wani jerin hare-hare da aka kai a yankin Sinai na kasar Masar. Wasu rahotannin sun ce dakarun tsaro 30 suka rasu sannan 50 sun jikata. Kafafan yada labaran Masar sun ce wasu 'yan bindiga suka afka wa wuraren bincike na sojoji da 'yan sanda a kusa da birnin Sheikh Suweid. An kuma samu fashewar bam a cikin mota. Tuni dai kungiyar IS ta yi ikirarin kai harin a yankin na Sinai da ke zama matattarar kungiyoyi masu kaifin kishin addini.