1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jami'in gwamnatin Libiya ya yi marabus

June 7, 2011

Kanal Muammar Gaddafi ya ce babu gudu babu ja da baya a faɗan da ƙasar sa ke yi da ƙawance na ƙasashen Duniya

Muammar GadhafiHoto: dapd

An bada rahoton cewa wani minista a cikin gwamnatin Kanal Muammar Gaddafi ya yi marabus.Al-Amin-Manfur wanda ke riƙe da matsayin ministan ƙwadago ya ajiye muƙamin a sa'ilin da ya ke halarta taron ƙungiyar ma'aikata na Duniya karo na 100 dake gudana a Jeniva.

Kamfanin dilanci labarai na AFP ya ambato wata wakiliyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar Libiyan a taron, ta na mai tabbatar da gaskiyar labarin.Wannan ba shi ne ba karo na farko da aka samu wani jam'in gwamnatin da ya arce daga ƙasar wacce ke fuskantar matsin lamba na ƙasashen duniya.A cikin jawabin da yayi wanda gidan telbijan na ƙasar ya yaɗa kanal Gaddafi ya ce ba zai bada kai ba bori ya hau. 'Zabi ɗaya gare mu ,zamu tsaya tsayin daka a ƙasar mu ko a mutu ko a yi rai baza mu yi saranda ba, ku tafi ku bar Libiya ga Libiyawa.Jume kaɗan bayan ya kammala jawabin sojojin NATO sun ƙara kai wasu sabbin hare hare ta jirage yaƙi masu saukar ungulu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal