1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

wani jirgin ruwa ya nitse a ƙasar Indiya

April 30, 2012

Mutane 35 daga cikin fasinjoji 250 na wani katafaren jirgin ruwa sun rasa rayukansu, lokacin wani hatsarin da ya afku a yankin arewa maso gabashin ƙasar Indiya.

An image made available on 1st April shows an overcrowded boat with African migrants who were rescued when migrant boats capsized in stormy seas off the coast of Libya arrives in Tripoli, Libya 29 March 2009 drowning many. Libyan authorities announced late 31 March 2009 that they had recovered 100 bodies but that many were still unaccounted for. Four migrant boats set sail for Italy with one breaking down near a Libyan oil platform, one is believed to have made it to Italy, one sunk and the location of the other is still unknown. The disaster is believed to be the deadliest migrant ship accident between North Africa and Europe in recent memory, an international migration official said. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Waɗanda ke neman tsallakowa Turai ne suka mituwa a ruwaHoto: picture-alliance/dpa

Wani ƙasaitaccen jirgin ruwa da ke ɗauke da fasinjoji kimanin 250 ya nitse a wani teku da ke yankin arewa maso gabashin Indiya bayan da ya ci karo da wata mahaukaciyar guguwa. Jami'an 'yan sanda Assam da ke zama jihar da hatsarin ya faru a cikinta sun bayyana cewar mutane 35 daga cikin fasinjojin sun rasa rayukansu, yayin da wasu 15 suka yi batad damo.

A halin yanzu dai, mutane 50 ne aka ceto daga cikin wannan jirgin da ya nitse a tekun Brahmapoutre. Jami'an agaji na ci gaba da bincike da nufin ceto wasu fasinjojin ko kuma gano gawawwakin waɗanda hatsarin jirgin ruwan ya ritsa da su. Wannan katafaren jirgin ya nufin gundumar Fakirganjan lokacin da ya ci karo da wannan mahaukaciyar guguwar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu