1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Wani sabon hari a kasuwa ya halaka rayuka a Sudan

September 27, 2024

Mayaka masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasra Sudan, sun kai wani hari da ya salwantar da rayukan fararen hula a wata babbar kasuwa da ke arewacin Darfur.

Inda aka kai wa hari a El Fasher da ke Darfur  na kasar Sudan
Inda aka kai wa hari a El Fasher da ke Darfur na kasar SudanHoto: AFP

Wani hari da myakan rundunar RSF da ke jayayya da gwamnati a Sudan suka kai wata kasuwa, ya kashe akalla mutum 18, kamar yadda majiyoyin lafiya ke tabbatarwa a yau Juma'a.

Da yammacin jiya Alhamis ne makyan suka afka wa kasuwar birnin El-Fasher da ke arewacin Darfur, inda lamarin ya kuma jikkata wasu da dama.

Hakan kuwa na zuwa ne yayin da shugabannin kasashen duniya ke neman ganin an kawo karshen yakin Sudan din, a babban taron bana na Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumomin asibitin koyarwa da ke birnin na El Fasher, sun ce wasu daga cikin mutanen da aka kashen, kone su aka yi wasu kuma ji musu munanan raunuka aka yi.

Kimanin mutum dubu 20 ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce aka yi asarar su a yakin na kasar Sudan.