Wani sabon nau'in cutar hanta na yaduwa a Turai
April 19, 2022Talla
A cikin wata sanarwa da ta fitar cibiyar kula da cututtuka ta Turai (ECDC) ta ce an samu karin yara da ke dauke da kwayoyin cutar ta hanta a kasashen Denmark da Ireland da Holland da kuma Spain. Cibiyar ta ECDC ta ce cutar da ke kama yara 'yan shekara daya zuwa shida na somawa da amai da gudawa da ciwon ciki.
A halin da ake ciki masana da kwararru na ci gaba da gudanar da bincike a duk cikin kasashen da aka ba da rahoton bullar cutar aa Turai da Amirka domin gano asalinta.