1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

050412 Grass Israel

Usman ShehuApril 5, 2012

Ana mayar da martani bisa sukar Isra'ila da wani shahararren marubuci ya yi kan ƙasar, inda yace lokaci ya yi da za a daina maida ita 'yar lele a duniya

Günter Grass , aufgenommen am 08.10.2010 auf der 62. Frankfurter Buchmesse in Frankfurt am Main.
Günter GrassHoto: picture alliance/dpa-Zentralbild

Jawabin da wani shararren marubuci ɗan ƙasar Jamus Guenter Grass, ya yi a kan ƙasar Isra'ila, a cikin wani littafin da ya wallafa, yanzu hakan sukar da ya yi wa Isra'ilan ta jawo martin dab-daban, inda wasu ke cewa yancin faɗar albarkacin baki ne, wasu kuwa na cewa kalaman da aka yi da na ƙyamar Yahudawane. Shi dai Guenter Grass ya soki Isra'ila inda yace tana mallake da makan nukiliya sanin kowa, amma tana yi wa ƙasar Iran barazanar banza.

Marubucin ɗan shekaru 84 a duniya, ya kalubalanci barazanar da kasar ta Isra'ila ke yi na kai farmaki ga tashoshin nukileyan ƙasar Iran, inda ya ce hakan wani yunƙuri ne na shafe jama'an kasar baki ɗaya. Guenter Grass a littafin nasa ya kara da cewa, ƙasar Isra'ila ita ce babbar barazana ga zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya, domin kuwa itace kaɗai ke mallake da makaman nukiliya. Guenter Grass, ya bayana a cikin littafin cewar lokaci ya yi da kasashen yammaci za su daina munafurci da son rai da suke sawa a dangane da batun Isra'ila, wace ita ma ta mallaki makaman nukleya. Julius Schoeps dake cibiyar nazarin alaƙar Turai da Yahudawa a Postadam cewa

Benjamin Netanjahu Firimiyan Isra'ilaHoto: AP

Martanin Yahudawa

"Ban yi imin cewa wannan batun na buƙatar babban mahawara. Guenter Grass a ra'ayina ya ɓata sunansa, kuma ya ɓata sunansa a matsayin wanda ya taɓa karɓar kyautar zaman lafiya ta Nobel. Ya kuma aikawa Yahudawa wani saƙo, na cewa Isra'ila itace ke da laifi, bisa gyamar da ake nuna mata. Wannan kalamen ba abune da za a lamunta da shi ba"

To sai dai wasu kuwa na ganin wannan kalamin ba wani abu bane, idan aka yi la'akari da cewa ko wane bil'adama yana da yancin fadin albarkacin baki, kuma kalaman da Bajamushe sharraren marubucin ya yi, babu gyamar Yahudawa kamar yadda wannan mutumin ke cewa.

Yancin faɗar albarkacin baki

"Wannan ba kyamar Yahudawa bace, marubucin ya soki gwamnatin Isra'ila ne, Idan dai wannan shine kalaman gyamar Yahudawa to rabin yan Isra'ila duk masu gyamar Yahudawane, domin suma kansu, suna sukar gwamnatin ta su"

Shugabar gwamnatin Jamus Angla Merkel da Firimiyan Isra'ila Benjamin NetanjahuHoto: AP

Kalaman da aka rubuta dai wasu Yahudawa sun fara yi mu saffara mai zafi innda suke nuna cewa har yanzu 'yar mitsitsiyar ƙasar tasu tana tana cikin hatsari.

Wannan kalaman na nufin shafe tarihin ƙasar Isra'ila. Mutun zai iya kallun kalaman nasa, a matsayin cewa har yanzu ɗorewar ƙasar Isra'ila yana cikin ayar tambaya. Wannan kuwa shine abin ya ƙara titar da duniya. A zahirance"

Shi dai Günster Grass wanda tsohon soja ne a zamanin yan Nazi. a cikin littafin nasa ya kira da a tura wata tawaga ta kasa da kasa mai cikaken inci domin ta binciki makaman da Isra'ilan ta mallaka. Abinda kuma ya tada hankali jami'an gwamnatin Yahudawa, inda suka yi Allah wadai da kalaman marubucin, yayinda gwamnatin Jamus ta ki ta ce unfum a kan batun.

Mawallafui: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Muhammed Abubakar