1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Wani mutum ya kashe kananan yara da adda a Uganda

April 2, 2026

Mutumin ya samu damar shiga makarantar Nursery ta "Gaba Early Childhood Development Program" ta hanyar basaja a matsayin daya daga cikin iyayen yaran. Sanna ya kulle makarantar kafin ya fara sassare yaran da adda.

Symbolbild Uganda Oppositionspartei Forum for Democratic Change
Dan sandan Uganda na saka ankwa a hannun wani mai laifiHoto: Dai Kurokawa/dpa/picture alliance

Jaridar Daily Monitor ta ruwaito cewa, shaidu sun ce wanda ake zargin ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin iyayen yaran, inda ya fara shiga ofisoshin makarantar kafin ya fara kai hari kan yara daya bayan daya.

Mai magana da yawun ‘yan sanda, Kituuma Rusoke, ya ce akalla yara hudu ne suka mutu a harin ba tare da an san dalilin harin ba. Sai dai wanda ake zargin, ya shiga hannun hukuma. Ba a cika fuskantar irin wadannan hare-haren ba a birnin Kampala mai yawan mutane kimanin miliyan uku.