1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka: Me ke janyo yawaitar juyin mulki?

Ehli David ARH/LMJ
December 15, 2025

Juyin muki a Madagascar da Guinea-Bissau, yunkurin juyin mulki a Benin: Afirka ta sha fama cikin makonni. Mai ya janyo yawaitar juyin mulki a nahiyar, akwai yiwuwar sake samun karuwarsa a shekarar da ke tafe ta 2026?

Guinea-Bissau | Bissau | 2025 | Janar Horta N'Tam | Sojoji | Juyin Mulki
Sojojin da suka kwace mulki a Guinea-Bissau karkashin jagorancin Janar Horta N'TamHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Juyin mulki biyu a kasa da makonni takwas da daya da ya ci tura a nahiyar Afirka, wannan wani abu ne da ba a taba gani ba a tarihin nahiyar da kuma ke zaman babban kalubale ga ci-gaba da ma dimukuradiyya. A watan Oktoba, sojoji a Madagascar sun kori shugaban kasa bayan zanga-zangar makonni.

A cikin watan Nuwamba, sojoji a Guinea-Bissausun kori shugaban kasa jim kadan bayan abin da suka ayyana da magudin zabe. A farkon watan Disamba, wasu sojoji da ya kira kansa kwamitin sake gina kasa wato CMR, ya sanar da kwace mulki a Jamhuriyar Benin. Amma daga karshe an dakile juyin mulkin, tare da kasashe abokan hulda musamman ma Najeriya.

Batun na kara rincabewa

Abubuwa Biyar tare da Sedik Abba

04:20

This browser does not support the video element.

A halin yanzu kasashe bakwai na Afirka na karkashin mulkin soja, galibi kasashen da ke amfani da harshen Faransanci. Mai yasa ake samun juyin mulki da yawa a Afirka a yanzu? Shin anya abin da ke faruwa, ba zai iya bazuwa cikin wasu kasahsen ba?

Gaba daya, ana iya lura da abubuwa uku da ke haifar da juyin mulki ko kuma yunkurin juyin mulki akai-akai: Matsin tattalin arziki da matsalar tsaro, kamar yadda ya addabi yankin Sahel tsawon shekaru da kuma tashin hankali da ke tattare da zabe. Zaben na kara shiga hadari, musamman lokacin da masu mulki ke son rike iko ko lokacin da cibiyoyin gwamnati ke da rauni wajen tsayar da gaskiya.

Akwai rashin gamsuwar sojoji, dangane da albashi ko yanayin aiki. Akwai masu tayar da zaune tsaye, wadanda ke son amfani da rashin gamsuwa da gwamnati da kuma ke janyo hankalin mutane ko kuma su kawo cikas ga huldar cibiyoyi.

Wasu kasashen na cikin hadari

Hasashen 2026 da siyasar matasan GenZ

02:19

This browser does not support the video element.

Masana na ganin cewa, yanzu haka akwai wasu kasahen Afirka da ke cikin hadarin juiyn mulkin,  misali Côte d'Ivoire da shugaban farar hula Alassane Ouattara ya fara wa'adinsa na huɗu. Wannan ya kasance mai cike da cece-kuce tsakanin 'yan adawa, kana kasar tana da tarihin tsoma bakin sojoji.

Haka ana sa ido kan Guinea: An shirya zabe a ranar 28 ga Disamba, domin kawo karshen matakin rikon kwarya bayan juyin mulkin wata Satumba 2021. Kungiyoyi kamar Tarrayar Afirka da ECOWAS, idan an yi juyin mulki sanarwa kawai suke yi na yin tir, amma da abin da ya faru. A Jamhuriyar Benin matakin da ECOWAS ta dauka na mayar da mulkin ga hambararren shugaban, ana gani watakila zai katse hanzarin masu yunkurin juyin mulkin.