1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Warkar Naira dubu a Nigeria

Yahouza sadissouOctober 23, 2005

Babbar Bankin Nigeria ta fuddo sabuwar warka ta Naira dubu a kasuwanin kasar

Sabuwar warka ta naira dubu a Tarayya Nigeria

Babbar bankin Nigeria ta bullo da warkaa daya ta Naira dubu a makon da ya gabata.

Rayoyi jama´a sun bambanta, a game da wannan Naira.

A yayin da wasu ke lalle marhabin da ita, wasun na sukar wannan mataki.

A ranar da ka yi bikin kaddamar da sabuwar Nairar, mataimakin gwamnan babar bankin Nigeria,El haji Shamsudden Usman, a hira da yayi da wakilin Radio DW na Abiua Ubale Musa, ya fadakar da jama´a bisa mahimancin bullo da wannan warka, dalili da ta na kawo sauki ta fannin daukar kudade, a cikin aljjuhwai ko jikkuna.

Mataimakin shugaban babar bankin, ya tabbatar da cewa, sabuwar Nairar ba ta karawa, kokuma rage darajar Naira na ainahi.

To saidai, duk da wannan jawabai na kwantar da hankali, wasu daga al´ummar kasa na cikin rudani.

Hajiya Mariam Ibrahim Babba, wata yar kasuwa da ta kawo ziyara aiki a nan gidan Redio DW, na daga masu wannan ra´ayi, inda a tunanin ta, warkar Naira dubun,koma baya ne, ga tattalin arzikin Nigeria.

A cen ma birninIkko jama´a na bayyana cewa basu ga anfani wannan sabuwar Naira ba, musamman ta la´akari da yadda su ke fama da talauci.

Rike Naira dubu a halin yanzu ya zama sai wane da wane a Nigeria inji wakilin mu na Ikko Umar Shehu Elleman.

A hannu daya kuma mutane na kokawa, ta yadda bayan bulo da sabuwar Nairar a ka fara samun yautar sace sacen yara.

To saidai sabanin wanann ra´ayi, a jihar Katsina, na yi hira da wasu yan kasuwa, na karamar hukumar Jibia.

Babba saadu mai kamus cewa yayi shi kam ya na lalle marhabin da sabuwar Naira, domin za ta kawo rangwame ga jiggilar kudade, daga wannan gari zuwa wancen, ko ma daga gida zuwa kasuwa, kokuma zuwa Banki.

A cewar El Haji Yushau mai Shada, na Jibia idan ma da wata Naira da darajar ta, ta fi dubu ya bullo da ita.

To abunda ke tabbas dai shine, a zahirin gaskiya takardar ta Naira dubu, ta sami al´ummomin Nigeria cikin halin kunci da talauc,i fata a an shine gwamnati, kamar yada ta bullo da Naira dubu, ta kuma bullo da matakan yaki da talauci, domin baiwa jama´a damar samun wannan Naira.